Wannan fassara ce ta ainihin rubutun Farisanci. Ainihin rubutu a Farisanci

بسم‌الله الرحمن الرحیم
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinƙai.

Zuwa ga mai girma Hossein Mozaffar! سلام علیکم (Aminci ya tabbata a gare ka);

Ina miƙa ta'aziyyar rasuwar mahaifiya mai daraja, mahaifiya mai sadaukarwa kuma mai haƙuri ta shahidai masu ɗaukaka Hassan, Ali da Reza Mozaffar (Allah Maɗaukaki Ya yarda da su) gare ka da sauran 'yan uwa masu girma da iyalai masu daraja na shahidai da masu sadaukarwa.

Wannan mace mai girman daraja kuma mai taƙawa, ta hanyar raino 'ya'ya muminai masu riƙon amana wajen kare martabar Juyin Juya Halin Musulunci, ta kai matsayi maɗaukaki na kusanci da Allah. Ana fatan ruhinta tsarkakakke, tare da ruhohi tsarkaka na 'ya'yanta shahidai, zai nutse cikin rahamar Ubangiji da yardarSa.

Sayyid Mojtaba Hosseini Khamenei