Wannan fassara ce ta ainihin rubutun Farisanci. Ainihin rubutu a Farisanci

بسم الله الرّحمن الرّحیم
Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.

ولاتَحسبَنَّ الّذینَ قُتِلوا فی سبیلِ‌اللهِ اَمواتاً بَل اَحیاءٌ عِندَ رَبِّهِم یُرزَقون
"Kuma kada lalle ka yi zaton waɗanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A'a, rayayyu ne a wurin Ubangijinsu, ana arzuta su." (Alƙur'ani, Ali Imran 3:169)

Cikin matuƙar baƙin ciki na sami labari mai raɗaɗi na shahadar Dakta Ali Larijani, Sakataren Babbar Majalisar Tsaron Ƙasa kuma wakilin Jagora a wannan majalisa, da ɗansa nagari da wasu daga cikin abokan aikinsa. Ya kasance mutum masani, mai hangen nesa, mai basira, mai riƙon amana, kuma mai ƙwarewa iri-iri a fagage daban-daban na siyasa, soja, tsaro, al'adu da gudanarwa. Kusan shekaru hamsin na taka rawa a matakai daban-daban na tsarin Musulunci sun mai da shi fitaccen mutum.

Babu shakka, kisan irin wannan mutum yana nuna girman muhimmancinsa da ƙiyayyar maƙiyan Musulunci a gare shi. Masu gaba da Musulunci su sani cewa zubar da waɗannan jinin a gindin babbar bishiyar tsarin Musulunci kawai yana ƙara ƙarfafa ta ne, kuma lalle kowane jini yana da diyyarsa, wadda dole ne masu laifi da suka kashe shahidan su biya nan ba da jimawa ba. Ina miƙa ta'aziyyata ta gaskiya game da wannan rashi ga matarsa mai daraja da sauran 'ya'yan wannan babban mutum, da kuma sauran danginsa, musamman Mai girma Ayatullah Amoli Larijani, kuma ina roƙon Allah, Gaskiya, جلَّ‌وعلا (Mai girma da ɗaukaka), Ya ɗaukaka darajojin waɗanda suka tafi.

Sayyid Mojtaba Hosseini Khamenei
26 ga Esfand, 1404