Wannan fassara ce ta ainihin rubutun Farisanci. Ainihin rubutu a Farisanci

باسمه‌تعالی
Da sunan Sa Maɗaukaki

Gaisuwa ga ’ya’yana ƙaunatattu;

Na karanta wasiƙunku masu cike da ƙauna. Ina godiya bisa ɗimbin alherinku, ku ɗaliban jami'a matasa masu ƙwazo, kuma ga dukkanku waɗanda kuka ɗora mini haƙƙi a wuyana, zan yi muku addu'a ta musamman.

A cikin wasiƙunku, da na matasa da ɗaliban jami'a da yawa waɗanda suke nuna wa wannan bawa mai ƙasƙanci alheri da ƙaunarsu, ƙuduri da azama da jin nauyin gina makoma suna haskakawa. Wannan alkawari mai ƙarfi amana ce mai matuƙar daraja, wadda ta samo asali daga makarantar Musuluncin Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) na gaskiya da gadon Khomeini Mai Girma da Khamenei shahidi (Allah Ya ɗaukaka matsayinsu mai daraja), kuma ita ce igiyar da ke haɗa mu da juna cikin «yin alkawari ɗaya».

Saboda wannan manufa, ku yi ɗamara gwargwadon ikonku da makamin ilimi da imani, da tsarkake zuci, da kusanci da Allah, da sanin koyarwar Alƙur'ani da Ahlul-Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) mai zurfi, kuma da ninkin aiki da ƙirƙira ku ƙara ƙarfi da izzar Iran ƙaunatacciya, domin albarkacin addu'ar shugabanmu mai jinƙai (Allah Maɗaukaki Ya gaggauta bayyanarsa mai albarka), tafiyar rundunonin da ke kan alkawari ɗaya zuwa kololuwar ci gaba da wayewar Musulunci da Iran ta tabbata cikin mafi kyau da gaggawa, in sha Allahu.

Sayyid Mojtaba Hosseini Khamenei
6 Aban 1405